Shugaban Amurka Donald Trump yana neman canza tsarin yadda ake baiwa mutane mafaka a Amurka, ciki har da shirin saka kudi ga wadanda ke cike takardun neman mafaka, yayin da gwamnatinsa ke kokarin dakatar da ci gaban kwararar da bakin haure ke yi ta kan iyakar Amruka da Mexico.
A wata takarda da aka fitar tun ranar Litinin, Trump ya nemi babban atoni janar da shugaban ma’aikatar harkokin wajen Amurka, su samar da sabbin dokoki cikin kwanaki 90.
Dokokin da za a samar sun hada da biyan kudi ga masu neman mafaka ko neman izinin yin aiki yayin da ake duba yiwuwar basu mafakar. Sai kuma hana izinin yin aiki ga duk masu neman mafakar da suka shigo Amurka ta barauniyar hanya. Sai kuma baiwa gwamnati har watanni shida domin yanke shawarar bayar da mafaka ko a a.
Haka kuma takardar Trump ta yi kira ga jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka su samar da jami’an da zasu ke duba duk wani batu da ya shafi tsoro ko tashin hankalin da ya sa ake neman mafaka, wanda ta haka ne masu neman mafaka a Amurka suke shawo kan jami’an AMurka su amince musu.