Trump Ya Bar Asibiti Bayan Yunkurin Hallaka Shi

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump

Ofishin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa, tsohon Shugaban kasar ya samu rauni a ka yau Asabar, amma yana “lafiya” bayan da aka harba bindiga a wajen da ya ke wani gangamin yakin neman zabe a Pennsylvania.

Ofishin yakin neman zaben Trump ya ce ana kulawa da dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Republican wani asibiti da ke garin Butler.

Trump ya je garin Butler da ke daya daga cikin jihohin da basu da tsayyen dan takara, domin gudanar da wani taro.

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da aka harbe shi a wurin yakin neman zabe

Kakakin ofishin yakin neman zaben Tump Steven Cheung ya fada a cikin wata sanarwa cewa, "Shugaba Trump ya godewa jami'an tsaro da jami’an agajin gaggawa saboda daukar mataki nan da nan yayin wannan danyen aikin, yana lafiya kuma ana duba lafiyarsa a wani asibitin gida."

Mutane sun ji kara masu kama da harbin kananan bindigogi kafin tsohon Shugaban ya kama gefen fuskarsa ya noke a bayan dogon teburin da yake tsaye yana magana. Nan da nan jami’an leken asiri suka yi wuf suka kakkange shi. Ana jin yana cewa “bari in dauko takalmina,” kafin ya mike tsaye, jami’an leken asiri suna kewaye da shi.

Mutane sun rungumi juna a wajen yakin neman zaben da aka harbi Trump.

An ga jini yana kwarara daga kunnensa na dama, ya kuma yi ta cewa, akai-akai, " jira." Daga nan ya daga hannu na dama ya tsira hannu yana nuna tsakiyar taron ya maimaita kalma guda daya sau uku.

Mai magana da yawun ma’aikatar leken asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban kasar yana cikin koshin lafiya. Wannan yanzu bincike ne na ma’aikatar tsaron, kuma za a fitar da karin bayani nan gaba."

Jami'an leken asiri suna kare Shugaba Donald Trump

Fadar White House ta aikawa manema labarai wata sanarwa cewa, Shugaba Joe Biden "ya sami bayanin farko game da abin da ya faru a taron tsohon Shugaba Trump." Bayan 'yan mintoci kadan, su ka ce manyan jami'an gwamnati da suka hada da shugaban hukumar leken asiri, da manyan hadimai da kuma sakataren tsaron cikin gida su na yi wa Shugaban kasar bayani a kan lamarin.

Wani Jami'in tsaro ya maida martani bayanda aka harbi Trump da bindiga a wajen yakin neman zabe.

Ofishin Mataimakiyar Shugaban kasar kuma ya shaida wa manema labarai cewa, Ana yi wa Mataimakiyar Shugaban kasar bayanin farko.

Babban Lauyan Karamar Hukumar Butler, Richard Goldinger ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa, dan bindigar da ake zargin ya mutu, kuma an kashe akalla mutum guda daga cikin wadanda su ka halarci taron.

Ku Duba Wannan Ma Ga Dukkan Alama An Harbi Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump a Pennsylvania