Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gudanar da gangamin yakin neman zabe karo na farko tun bayan da ya tsallake rijiya da baya yayin da aka yi yunkurin kashe shi a makon da ya gabata, inda ya koma jihar Michigan mai muhimmanci wajen cin zabe tare da mataimakinsa JD Vance.
"Da taimakon Allah madaukaki na ke tsaye a gabanku a yau," a cewar Trump." An cire farin bandejin da aka sanya masa a kunne, yanzu an sanya masa wani mai launin fatar bil’adama. Ya kara da cewa "da yanzu ba na tare da ku."
Sanata JD Vance daga jihar Ohio ya hadu da Trump don gangamin yakin neman zaben na farko tun bayan da aka tabbatar cewa sune 'yan takarar jam’iyyar Republican a babban taron jam'iyyar da aka yi a Milwaukee.
Michigan na daya daga cikin jahohin da ke da muhimmanci wajen cin zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba. Trump ya lashe zabe a jihar da kyar da kuri’u sama da 10,000 a shekarar 2016, amma dan jam’iyyar Democrat Joe Biden ya sauya hakan a shekarar 2020, inda ya lashe zaben da tazarar kuri’u 154,000 a lokacin zaben da ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Zaben Vance da Trump ya yi, a wani bangaren ya yi ne da nufin samun goyon bayan masu kada kuri'a a jihohi kamar Michigan, Pennsylvania, Wisconsin da Ohio, wadanda suka taimaka wa Trump a nasarar da ya samu a shekarar 2016. Vance ya ambaci wadannan wuraren musamman a lokacin jawabinsa na amincewa da zabarsa da aka yi a matsayin mataimakin Trump a taron, yana mai jaddada yadda ya girma a cikin talauci a Ohio, ya kuma yi alkawarin cewa ba zai manta da rukunin ‘yan kasar ma’aikata ba, wadanda “ayyukansu su ka koma kasashen waje sannan aka tura yara zuwa yaki.”
‘Yan sa'o'i kafin ya hau kan dandamali, magoya bayan Trump sun yi cincirundo a kan titunan birnin Grand Rapids, suna jiran jawabin tsohon shugaban. Tun da safiyar Juma’a magoya bayansa su ka fara jan layi a wurin, ya zuwa yammacin ranar Asabar, layin ya kai kusan mil daya daga kofar shiga filin wasa na Van Andel Arena mai dauke da kujeru 12,000.
An kuma baza ‘yan sanda sosai a birnin Grand Rapids, yayin da wasu su ka yi ta sintiri a kan dawakai da kekuna. Tsauraran matakan tsaro da aka sanya a wajen wurin taron sun sa wasu kasancewa cikin yanayin fargaba, inda wasu da suka halarci taron suka bayyana cewa jiragen sama marasa matuki da suka yi ta shawagi a sama sun figitasu.