Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Alhamis ya yi barazanar kakabawa Tarayyar Turai harajin kashi 200% kan ruwan inabi, shampen, da sauran nau’ukan giya da ake samarwa a cikin kasashe 27 na tarayyar ta EU.
Wannan na zuwa bayan da EU ta sanya abin da Trump ya kira "mummunan harajin kashi 50%" kan giya da ake sarrafawa a Amurka.
Trump ya fada a shafinsa na Truth Social cewa EU na daga cikin "mafi munin hukumomin haraji da cinikayya a duniya." Ya ce kungiyar an kafa ta a shekarar 1993 da manufar "kwarar Amurka ta fuskar tattalin arziki."
Daga baya, wani dan jarida ya tambaye shi a Fadar White House ko zai iya sassauta barazanar harajin da ya ke yi wa kawayen Amurka na duniya, sai ya amsa da cewa:
"An jima ana kwarar mu tsawon shekaru, ba za mu sake amincewa da haka ba.” Trump ya ce.