Tsohon Shugaban Kasa Donald Trump ya shiga wata motar diban shara da aka rubuta sunansa a jiki inda ya yi kokarin jan hankalin jama’a kan wata magana da Shugaba Joe Biden ya fada a ranar da ta gabata.
Yayin da yake magana da manema labarai a filin jirgin sama a Green Bay, Wisconsin, Trump ya tambaya, “Yaya kuke ganin motar sharata?”
Sanye da rigar kare lafiya mai launin lemo da rawaya Trump ya fada cikin shagube cewa shigarsa cikin motar sharar mataki ne "na girmama Kamala Harris da Joe Biden."
Trump da wasu ‘yan jam’iyyar Republican suna kokarin sauya ce-ce-ku-cen da ake yi bayan da wani mai wasan barkwanci a taron Trump na karshen mako ya yi magana mara dadi kan Puerto Rico, inda ya kira tsibirin wani wuri na shara mai iyo.
Kakakin Trump ya ce tsohon shugaban kasar baya goyon bayan kalaman na Tony Hinchcliffe.
Trump ya yi amfani da wasu kalamai da Shugaba Joe Biden ya yi a ranar Laraba wadanda su ma suka janyo ka-ce-na-ce inda ya ce, “sharar da nake gani tana yawo ita ce ta magoya bayansa (Trump)”
Daga baya dai Biden ya ce ba abin da yake nufi ba kenan, amma ga dukkan alamu bakin alkalami ya riga ya bushe.