Trump Ya Sanar Da Sabon Sakataren Tsaron Amurka

Shugaba Donald Trump tare da Patrick Shanahan

Sabon sakataran harkokin tsaron Amurka na riko Patrick Shanahan zai fara aiki a ranar daya ga watan Janairu 2019, wanda zai canji Jim Mattis da ya ajiye aikinsa saboda adawa da janye sojojin Amurka daga Syria.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa karamin sakataren tsaron Amurka Patrick Shanahan zai zama shugaban ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon daga ranar daya ga watan Janairu, domin cike gurbin Jim Mattis da ya sanar da ya yin murbus a makon da ya gabata.

Trump ya sanar da wannan ne a cikin wani sakon Twitter da ya aike, yana mai cewa daga daya ga watan Janairun 2019, kwararren mataimakin sakataren tsaro Patrick Shanahan, zai fara aiki a matsayin sakataren tsaro na riko, lamarin da zai sa Mattis ya ajiye aiki watanni biyu kafin lokacinsa.

Shanahan tsohon shugaban kanfanin jirgin Boeing, ya zama mataimakin sakataren tsaron Amurka a shekarar 2017.

A ranar juma’a ne Mattis ya kai takardarsa na yin murabus kuma yace zai ajiye aiki a ranar 28 ga watan Faburairu 2019.

Shawarar ajiye aiki da sakataren tsaron ya dauka ta biyo bayan sanarwar da Trump ya yi zai janye sojojin Amurka dubu biyu daga Syria, wani mataki da Pentagon ta kalubalanta.