Trump Ya Musunta Zargin Cohen Kuma Ya KIra Shi Makaryaci

Donald Trump

Donald Trump

Bayan da tsohon lauyan Trump ya shaidawa kwamitin majalisar dokokin Amurka cewa Trump din "dan wariyar launin fata ne, mayaudari," shugaban na Amurka ya fada a yau Alhamis cewa zancen da Michael Cohen ya fadi ba gaskiya bane kuma ya sha yin karya.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Vietnam bayan taron kolin da ya yi da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, Trump ya kara jaddada cewa babu wata alaka da ta hada wadanda suka yi mashi yakin neman zabe da kasar Rasha a lokacin zaben shekarar 2016.

Cohen ya shaidawa kwamitin na bincike a jiya Laraba cewa ba shi da wata hujja a hannu dake nuna cewa Rasha da ‘yan kemfen din Trump sun tattauna, amma yace yana kyautata zaton an yi hakan.

Cohen ya kuma ce ya taba jin wata tattaunawa tsakanin Trump da dansa, Donald Trump Jr. kuma yana kyautata zaton a kan batun ganawar da ta faru tsakanin manyan jami’an kemfen din Trump da wani lauyan kasar Rasha dake da alaka da gwamnatin kasar a shekarar 2016, a dogon benen Trump dake New York.