Trump Ya Ki Amincewa Da Tayin Mai Kwarmata Bayanan Sirri

Shugaban Amurka Donald Trump, da ke fuskantar binciken da mai yiwuwa ya kai ga tsige shi, ya ce rubutattun amsoshin da mutumin da ya kwarmata bayyanan cewa ya tursasa Ukraine ta binciki daya daga cikin babban abokanan hamayyarsa a zaben shekarar 2020, wato tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden, sam ba za su gamsar ba.

A jiya Litinin, Trump ya shiga shafinsa na Twitter, ya mayar da martani game da batun mai kwarmata bayanan sirrin, inda ya ce ya zama "dole ya gurfana domin ya ba da shaida, bai kamata a lamunci rubutattun amsoshi ba.”

Shugaban na Amurka ya kuma kira binciken tsige shin a matsayin na “damfara.”

Martanin Trump kan yunkurin da ‘yan majalisar wakilai ke yi na tsige shi, na zuwa ne kwana guda bayan da wani lauya a Washington mai suna Mark Zaid, ya ce, mutumin da yake wakilta – wanda shi ya kwarmata bayanan da ba a bayyana sunansa ba, ya amince zai amsa tambayoyin 'yan jam'iyyar Republican da ke goyon bayan Trump, a rubuce.

Su dai ‘yan jam’iyyar ta Republican sun ce ba su yarda da wannan tayi ba.