Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa birnin Baltimore da ke gabashin Amurka mai yawan bakar fata, wanda a kwanakin baya ya kira wuri mai cike da kazanta da beraye da yawan kwari, inda babu wani dan Adam da ke sha’awar zama.
Trump ya je wurin a jiya Alhamis ne domin yin jawabi a wurin taron shugabannin jami’iyar Republican a Majalisar Tarayya.
Kafin ya bar fadar White House, Trump ya yi watsi da tambayoyin da ‘yan jarida suke masa cewa me zai fada wa mazauna birnin, sai dai kawai ya ce za a samu maraice mai cike da nasarori.
Gabanin ziyarar shugaban kasar, wani gungun masu fafutuka ya shirya gudanar da zanga zanga na kalubalantar wariyar launin fata da akidar fifita farar fata da yaki da girman kai da ma sauyin yanayi, kamar yadda masu shirya zanga zangar su ka fada wa jaridar The Baltimore Sun.