Trump ya Gayawa Amurkawa Su Kuka da Alkalin da Ya Dakatar da Dokarsa Idan Wani Abu Ya Faru

Donald Trump shugaban Amurka wanda ya kafa dokar hana al'ummar kasashe bakwai shigowa Amurka

Shugaba Donald Trump, yana gayawa Amurkawa cewa "idan wani abu ya faru", suyi kuka da alkalin da ya dakatar da aiki da dokar da ta hana balaguro zuwa Amurka daga al'umar kasashe bakwai wadanda akasarin jama'ar su musulmi ne.

A daya daga cikin sakonnisa ta shafin Tweeter a jiya Lahadi, shugaban yace "Gaskiya na gaza fahimtar yadda alkali zai jefa kasarmu cikin hadari."

A wajajen karshen makon jiya ne, alkalin wata kotun Amurka James Roberts a jahar Washington ya dakatar da aiki da dokar shugaban kasar na wucin gadi. Sannan a jiya Lahadin, kotun daukaka kara shiyya ta tara dake San Francinsco taki amincewa da bukatar da gwamnatin Trump ta gabatar na neman kotun ta bada izinin a ci gaba da aiki da dokar.

A ci gaba da sakonnin Tweeter a jiya Lahadi, Mr. Trump yace ya umarci ma'aikatar tsaron cikin gida ta "binciki masu shigowa Amurka sosai". Ya kara da cewa alkalin ya tsananta aikin masu kula da shige da fice".