Wata kotun daukaka kara a birnin San Francisco nan Amirka ta yi watsi da bukatar gwamnatin Trump cewa nan take ta maido da umarni shugaban data haramtawa yan kasashe bakwai zuwa nan Amirka.
Da sanyin safiyar Lahadi kotun ta bukaci gwamnatin Trump da kuma jihar Washington da su gabatar da karin hujoji ko kuma dalilansu akan wannan batu gobe Litinin idan Allah ya kaimu.
Asabar da dare ma’aikatar shari’a ta daukaka karar hukuncin da wani alkali ya yanke na yin watsi da umarnin shugaban.
Umarni ko kuma dokar shugaba ta haddasa rudami tsakanin hukumomin gwamnati da kotu a yayinda ta hadasa zanga zanga a biranen Amirka da dama da kuma wasu kasashen waje. Wannan al’amarin ne yasa aka kori Atoni Janaral Sally Yates a saboda taki da kare doka ko kuma umarnin shugaban