Shugaban Amurka Donald Trump yana ziyara a Birtaniya inda yake ganawa da iyalan masarautar kasar, sannan ana sa ran zai yi wata liyafar tare da Firai ministar Theresa May mai barin gado.
A yau Litinin, Trump da uwargidansa Melania, suka samu tarbar Sarauniyar Ingila Elizabeth da Yarima Charles a lokacin da suka isa fadar Buckingham a jirgi mai saukar ungulu.
Kafin ya tashi daga nan Washington, Trump ya ce tafiyar tasa “ za ta kayatar sosai” kuma yana tunanin cewa Amurka da Birtaniya suna da damar da za su yi aiki tare wajen kulla “gagarumar yarjejniyar kasuwanci” nan ba da jimawa ba.
Ziyarar ta shugaba Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Birtaniya ta ke cikin rudanin siyasa. Firaiminista May ta sanar a watan da ya gabata cewa za ta sauka daga mukaminta bayan da ta gaza cimma yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai.