A ranar Talata, tsohon shugaban kasa Donald Trump ya kara yada jita-jita marar tushe cewa, ‘yan gudun hijirar Haiti a jihar Ohio da ke Amurka na sacewa tare da cin dabbobin cikin gida, inda ya maimaita a wata muhawara ta talabijin, irin kalaman batanci da kyamar baki da ya ke yadawa a duk lokacin yakin neman zabensa.
Jami’ai sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa ‘yan gudun hijirar Haiti da ke cikin al’ummar Ohio su na yin hakan. Sai dai yayin muhawara da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, Trump ya yi magana musamman a Springfield na Ohio, garin da shi ne ke tsakiyar zargin, yana mai cewa bakin hauren sun kwace garin.
Ya ce, “Su na cin karnuka. Su na cin maguna. Su na cin dabbobin mutane da suke zaune a wurin.”
Harris ta kira Trump “mai tsattsauran ra'ayi” kuma ta yi dariya bayan kalaman nasa. Masu gudanar da muhawarar sun bayyana cewa jami’an birnin na Ohio sun ce zargin ba gaskiya ba ne.
Kalaman na Trump sun sake maimaita maganganunsa na yakin neman zaben shi wanda ya hada da na abokin takarar shi sanatan jihar Ohio JD Vance da sauran ‘yan Republicans. Zargin ya ja hankalin mutane da dama cikin makon nan bayan da Vance ya wallafa a shafin sa na sada zumunta cewa, ofishin sa “ya samu takardun korafe korafe” akan baki ‘yan kasar Haiti su na sace dabbobin mutane da ke debe musu kewa. Vance ya amince cewa, akwai yiwuwar cewa duk zarge zargen su kasance karya.”
Jami’ai sun ce babu wani sahihi ko cikakken bayanai akan wannan zargin, ko da yake Trump da tawagarsa su na amfani da wadannan batutuwa wajen dada nuna wariyar launin fata ga baki bakaken fata ko wanda ba farare zalla ba ne.