A cikin watan Nuwamba mai zuwa ne masu jefa kuri’a anan Amurka zasu jefa kuri’a na tsakiyar lokaci ko wa’adi na wakilan Majalisar dokoki, wanda yanzu haka dai majilisun dokoki biyu na da rinjayen jamiyyar Republican, sai ga bisa dukkan alamu malisar Dattijai tana cikin rudu da damuwa.
Domin ko sakamakon wannan zaben na iya kawo wa shugaba Donald Trump nakasu, kuma yanzu haka shugaban ya fara lura da hakan.
Ba mamaki wannan yasa a wajen wani gangami makamancin na yakin neman zaben da shugaban ya fara a Washington da Michighan, Trump ya fara magana da kakkausar lafazi akan jamiyyar adawar sa ta Democrat, yana cewa muddin akasa wa Democrat kuri’a a watan nuwamba to ku kwana da sanin cewa bakin iyakar kasar ku yana bude wagaga, sai kuma masu aikata laifuffuka.
Kamar yadda wani shafin yanan gizo mai suna Real Clear, ke cewa jamiyyar Democrat tana da alamun galaba akan Republican da maki 7