Manyan jami’an hukumomin tsaro na Amurka sun kame bakunansu, sun ki cewa uffan akan rahottanin da ake bayarwa da ke cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya bada umurnin akai wa Iran hari jiya Alhamis, amma kuma daga bisani ya janye umurnin ba tare da gabatar da wasu dalilai ba.
Jaridar New York Times tace da farko shugaba Trump ya bada umurnin a kai farmakin jiragen sama akan wasu sansanonin da suka hada da wuraren da Iran ke girke makamanta masu linzamai da sauransu, kafin ya canza ra’ayinsa.
Ita ma jaridar Washington Post da wasu kafofin labarai duk sun tabattar da cewa shugaba Trump ya bada umurnin a kai harin na ramuwar gayya, bayan da Iran ta kakkabo wani jirgi mara matuki na Amurka da ke shawagin leken asirai daga samaniya.
Shima kamfanin dillacin labarai na Reuters ya tabattarda cewa Iran ta sami sakon Trump, jiya da dare daga hukumomin kasar Oman, inda aka sanar da ita cewa ana dab da kawo mata wannan farmakin.