Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ba zai iya jira makwanni ko watanni ko kuma shekaru kafin fitar da sakamakon zaben watan Nuwamba ba, saboda wasu matsaloli da yake hasashen suna tattare da kada kuri’a ta gidan waya.
Trump ya fadawa manema labarai a jiya Alhamis da rana a fadar White House cewa, baya so ya jira tsawon watanni uku kafin a gano kuri’un da aka kada sun bace, wato zabe bai yi ma’ana ba ke nan. Masu kaifin hankali sun san abin da nake fadi, amma marasa wayau basu sani ba.
Da safiyar jiya Alhamis, Trump ya bada shawarar jinkirta zaben shugaban kasa, yana wani zargi a sakon twitter ba tare da kawo shaida ba cewa, zaben ta gidan waya da ake dadewa kafin a kirga, zai sa zaben shugaban kasa na shekarar 2020 ya kasance da yawan rashin adalci da magudi.
Shugaban dan jami’iyar Republican ya kara da cewa, wannan abu zai zamewa Amurka babban abin kunya. Yana mai cewa a jinkirta zaben har sai jama’a sun samu daman kada kuri’a cikin kariya da natsuwa.
Da take maida martani ga sakon Twitter, kakakin majalisar dokoki Nancy Pelosi ta yi nuni da ayar dokar Amurka da ta baiwa majalisar dokoki hurumin fitar da ranar zabe da lokaci da masu zabe zasu kada kuri’ar su kuma a wannan ranar ce za'a gudanar da zabe a fadin Amurka baki daya.