Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna So Mutane Su Gamsu Da Sahihancin Rigakafin COVID-19 - Fauci


Dr Fauci na Amurka
Dr Fauci na Amurka

Yayin kasashen duniya suka tsunduma wajen aikin neman rigakafin Covid-19, masana na ci gaba da yi wa mutane gargadi kan kin amincewa da rigakafin.

Fitaccen kwararren masanin cuttutuka masu yaduwa na Amurka, ya ce, yayin da ake samun nasara mai ma’ana a game da samar da rigakafin cutar COVID-19 a fadin duniya, ya zama wajibi mutane su kasance sun gamsu da sahihancinta.

A wata hira ta musamman da ya yi da kamfanin dillacin labarai na Associated Press a daren Talata, ma’aikacin cibiyar lafiya ta kasa, Dr. Anthony Fauci, ya ce, aikin samar da maganin cutar na sauri, lura da yadda ake bukatar maganin cikin gaggawa.

Sai dai ya ce, mai yiwuwa, hakan zai iya sa a nuna damuwa kan rashin ingancin maganin.

Yadda ake yi wa wata gwanin rigakafin Covid-19
Yadda ake yi wa wata gwanin rigakafin Covid-19

Fauci ya ce, sai an yi aiki tukuru wajen wayar da kan al’uma don a kwantar musu da hankali.

“Muna so mu tabbatar cewa ba mu boyewa mutane komai ba, muna kuma so su gamsu da cewa, saurin da ake yi na neman maganin ba zai hana a tabbata an kiyaye lafiyar jama’ar ba, sannan ba zai sa a karya ka’idojin da binciken kimiyya ya shimfida ba

Ya zuwa yanzu cutar ta Covid-19 ta kama akalla kusan mutum miliyan 17, ta kuma kashe sama da 650,000 a duk fadin duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG