Trump Na Shirin Halartar Taron NATO

Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

A wannan makon shugaban Amurka Donald Trump zai je birnin London don halartar taron kungiyar tsaro ta NATO, yayin da ake cigaba da takaddamar tsige shi a gida Amurka da ya shiga wani sabon babi.

“Wannan abu ba zai kare ba, saboda suna son su yi abinda suke so ne,” Shugaba Trump ya fadawa manema labarai yayin da yake barin fadar White House, yana nufin binciken tsige shi da ‘yan jam’iyyar Demokrat suke yi.

Yayin da ‘yan Demokrat za su fara sauraran bahasi kan rubuta kudurin dokar tsige shugaba Trump ranar Laraba, dayawa daga cikin shugabanin kungiyar tsaro ta NATo suna sane da irin kalubale da shugaba Trump yake fuskanta a gida na tsige shi.

Sauraron bahasin tsigewa “yana cin lokacin da ya kamata a yiwa al’umma aiki sosai” ga shugaban kasa da kuma hadimansa na kusa a cewar Gary Schmitt.