Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na sake yin nazari akan sababbin matakai yadda jihohin kasar za su sake bude harkar kasuwanci, makarantu da majami’u, yayin da jihohi da dama suka nuna sha’awar yin hakan.
Hukumomin Amurka sun bayyana cewa, Hukumar hana yaduwar cutattuka wato CDC ce ta samar da jadawalin da za’a bi a fannoni daban daban.
Kafafen yada labarai na Amurka da suka ga jadawalin, jiya Litinin sun bayana cewa, ya hada da rurrufe wuraren cin abinci a ma’aikatu, amfanin da takardun jerin zabin abinci da za a yi amfani da su sau daya a gidajen cin abinci, da kuma dakatar da kade-kade da wake-wake a wararen ibada. Jami’ai sun ce jadawalin na iya canjawa.
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Texas Greg Abbott ya ce daga ranar jumm’a zai ba da dama a fara bude harkokin kasuwanci inda zasu bari kashi 25 cikin dari na abokan kasuwancinsu su shiga shagunan a lokaci guda.