Ana ci gaba da samun karin jIhohin Amurka da ke kawar da wasu daga cikin matakan takaita harkoki, saboda dakile cutar coronavirus.
Hakan na faruwa ne yayin da gwamnatin Trump take sake nazarin tsarin yadda jihohi za su iya bude harkokin hada-hada, da makarantu da wuraren ibada sannu a hankali.
Jami’an Amurka sun ce tsarin, wanda cibiyar yaki da cututtuka masu yado ta gabatar, ya bayyana dalla-dallar yadda za a sake bude harkoki a yanayi daban- daban.
Kafafen yada labaran Amurka da suka ga tsarin da ake shirin gabatarwa din, a jiya Litinin sun ce tsarin ya hada da rufe duk wani dakin cin abinci da ofisoshin aiki.
Sauran tsare-tsaren sun hada da yadda za a yi amfani da cokala da wuraren sa abinci na zubarwa bayan an gama a wuraren sayar da abinci, da dakatar da wakoki a yayin harkokin ibada.
Jami’an sun ce ta yi wu a sake garanbawul ga tsarin nan gaba.
Facebook Forum