Shugaban Amurka Donald Trump na jefa ayar tambaya kan yanayin hankali da tunanin abokin karawarsa a zaben watan Nuwamba, wato tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, bayan haka ya na nuna cewa bai cancanta ya zama shugaban kasa ba.
A wata hira da aka yi da shi a wani shiri na musamman na ranar Lahadi a gidan talabijin din Fox News inda Trump ya caccaki tsohon mataimakin Shugaban, ya nuna cewa Biden bai iya hada jumla biyi a bayaninsa.
Zasu gabatar da shi a wuri. Zai tashi ya je, ya maimaita abu, za su yi masa tambayoyi. Zai yi karatu daga na’urar nuna karatu daga nan ya sake labewa, a cewar Trump. Ku fada min ko Amurkawa zasu so su samu irin wannan mutumin a zamanin da mu ke fuskantar matsaloli, wasu kasashen na neman hanyar yi mana illa.
Kwamitin yakin neman zaben Trump ya saki wasu tallace-tallace masu jefa ayar tambaya a kan ko yanayin hankalin Biden mai shekaru 77, wanda zai zama shugaban Amurka wanda ya fi yawan shekaru idan ya yi nasara a zaben ranar uku ga watan Nuwamba kana aka rantsar da shi a watan Janairu mai zuwa, ya fara gushewa ko a'a. A halin yanzu dai Trump mai shekaru 74 shi ne shugaba mafi yawan shekaru a Amurka.