"Ba zai tsaya nan ba," abin da Jakadiya Nikki Haley ta gaya ma kafar labarai ta CNN kenan jiya Lahadi. Ta kara da cewa, "in da bukatar ya kara, zai karan."
To amma Haley da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson, sun yi bayanai masu cin karo da juna game da muhimmancin kawo karshen gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriyar.
"Ba a yanke shawara ba tukunna kan irin matakin da za a dauka a siyasance game da Assad a matsayinsa na jagoran gwamnatin," a cewar Haley wadda ta kara da cewa, "Idan ka yi la'akari da take-takensa, idan ka kuma dubi al'amarin da ake ciki, sai ka ga da wuya a iya samun gwamnati a Siriya tsayayya kuma mai zaman lafiya muddun Assad ne ke mulki. Sauyin gwamnati wani abu ne da mu ke tsammanin zai faru," a cewarta.
To amma Tillerson ya ce abin da Amurka ta fi bai wa fifiko a Siriya shi ne batun yin galaba kan ISIS.
"Ya na da muhimmanci mu fayyace abin da mu ka baiwa fifiko," abin da Tillerson a shirin Face the Nation kenan na kafar labarai ta CBS. Ya kuma kara da cewa, "Kuma mun yi imanin cewa abu na farko shi ne fatattakar ISIS."