Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Zata Gurgunta Tsaro A Birnin Baltimore


Jeff Sessions
Jeff Sessions

Gwamnatin Trump ta Bukaci a jinkirta saka hannu a kan yarjejeniyar gano tushen nuna bambamcin launin fata a ma’aikatar 'Yan sandan dake garin Baltimore,

Atoni Janar na Amurka kuma ministan shari’a baiji dadin yadda hukumar 'Yan Sanda ta birnin Baltimore ta yanke hukuncin mutunta yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin Barack Obama ba.

Duk da cewa Atoni Janar Jeff Session, yana ganin cewa yarjejeniyar zata “gurtgunta” tsaro a birnin, Magajiyar garin Baltimore Catherine Pugh, bata amin ce da matsayar Jeff Sessions ba, a ganinta yarjejeniyar zata karfafa tsaro a birnin na Baltimore.

A ranar Jumma’a wani alkalin kotun gunduma ta Amurka James Bredar ya amince da yarjejeniyar, har yake cewa shirin “Cikakkiya ce Wadatacciya kuma mai tsari.” Gwamnatin Trump ta nemi Bredar da ya jinkirta a saka hannu a kan yarjejeniyar domin ta sami cikakken lokacin duba yarjejeniyar wacce aka tsara da nufin gano tushen nuna bambamcin launin fata acikin ma’aikatar ta Yan sandan dake garin Baltimore, mai tazarar kilomita 65, a Arewacin Washington.

An cimma wannan yarjejeniyar ce a kwanakin karshe na Gwamnatin Barack Obama bayan Binciken da gwamnatin tarayya tayi ya gano cin zarafin zarafi wanda ya zama ruwan dare a rundunar Yan sanda na Balrimore, wanda ya hada da Tsaida mutane ba bisa doka ba da kuma amfani da karfi akan Bakaken fatar Amurka.

Dokar ba wata aba bace face kwantiragi ne tsakanin Ma’aikatar Yan sanda da kuma Ma’aikatar Shari’a ta tarayya domin samun nasarar yin gyare gyare karkashin kulawar gwamnatin tarayya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG