Gwamnatin Amurka ta dakatar da yunkurin ta na takurawa kamfanin twitter da ya bayyana mutanen da suka kirkiri shafukan dake tsanantawa ga Shugaban kasa Donald Trump, kamar yadda kamfanin sada zumuntar ya bayyana.
A madadin haka, kamfanin na Twitter yace zai ajiye karar gwamnatin Amurka da tayi a kotun Gwamnatin tarayya na kokarin takura su da ake son yi da su bayyana wadanda suka bude shafukan.
Kamfanin na Twitter ya shigar da karar ne kwana daya, inda tace gwamnati ta wuce gona da iri akan huruminta na aikowa da sammace domin bayyana masu wadannan shafuka.
Karar dai ance ma’aikatar Tsaron cikin gida da kuma ma’aikatar fasakwauri da kare iyakar kasa na son sanin wanda ya kirkiri shafin twitter mai suna @ALT-USCIS.
Shafin dai ya bayyana kansa ne a matsayin “Mai jajircewa kan harkokin Bakin haure” wanda ya kirkiri shafin ya bayyanawa manema labarai cewa tsofaffi da kuma ma’aikatan hukumar Bada izinin zama da kuma bakin haure wato USCIS a takaice ne dake aiki a yanzu suke kula da shafin wanda Hukumar ma’aikatan tsaron kasa ke dubawa.
Shafin dai d’aya ne daga cikin wasu shafukan da aka bude wanda ma’aikatan gwamnatin tarayya da basa murna da gwamnatin Trump suka bude a matsayin Wani zabin aturance “Alternative”
Facebook Forum