Trump Na Duba Yiwuwar BaiwaTillerson Mukamin Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Shugaban kamfanin mai na Exxon Mobil, Rex Tillerson

Shugaban kamfanin mai na Exxon Mobil, Rex Tillerson, shi ne mutum na gaba-gaba da aka saka a jerin mutunen da ake tsammanin za a baiwa mukamin Sakataren harkokin wajen Amurka a sabuwar gwamnati mai shigowa.

Kafofin yada labaran Amurka da dama sun ruwaito cewa wata majiya da ba a bayyana sunanta ba, ta ce nan ba da jimawa ba za a ayyana Tillerson a matsayin wanda zai rike mukamin na Sakataren harkokin wajen Amurka.

Sai dai masu fada a ji a bangaren Trump sun ki tabbatar da ko Tillerson shi zai kasance zabi na karshe, amma kuma an ji shugaban mai jiran-gado Donald Trump ya na yaba shi a lokacin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Fox News.

“A gani na, babban amfaninsa shi ne ya san mafi yawan mutanen da ake damawa da su, ya sansu su sosai, ya sha yin harkokin cinikayya a Rasha.” In ji Trump.

Yanzu Tillerson ya shiga sahun su Mitt Romney da ya yi takara a shekarar 2012, a matsayin wadanda ake sa ran baiwa wannan mukami.

A da akwai tsohon Magajin Garin New York, Rudy Giuliani, amma a ranar Juma’a aka cire sunansa daga jerin sunayen.