Trump, Harris Sun Kara Kaimi Wajen Caccakar Juna

Kamala Harris, (Hagu) Donald Trump (Dama)

Kalaman manyan 'yan takarar biyu na zuwa ne yayin da Amurkawa ke shirin kada kuri'a a ranar 5 ga watan Nuwamba.

‘Yar takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi gargadin cewa Donald Trump na jam'iyyar Republican zai nemi "kirkirar dokar" da za ta haifar da koma baya ga bakaken fata.

Ta kuma yi alkawari a wata hira da mai gabatar da shirin rediyo, Charlamagne the God, cewa za ta yi kokarin samar da dokar da za ta magance yadda ake nuna banbanci wajen aiwatar da doka.

Trump ya zargi manufofin shige da fice na Harris da "lalata" al'ummomin bakaken fata da al’umomin Latino yayin da yake gudanar da wani gangamin da daddare a Atlanta.

Harris ta ce ana nuna wa babake bambanci launin fata da wariya a rayuwarsu ta yau da kullum - wajen mallakar gidaje, kiwon lafiya, ci gaban tattalin arziki har ma da zabe — tana mai cewa babu wanda ke da hujja da zai ki fita don kada kuri'a.

Trump ya nace cewa bakin haure na shafar rayuwar bakaken fata ta hanyar kwace musu ayyukan yi.

Ya kuma kwatanta shirin da Shugaba Biden da Mataimakiyarsa Kamala Harris suka samar akan iyakar Amurka a matsayin wani mataki na watsawa al’ummar bakaken fata da na Latino kasa a ido.

Kalaman manyan 'yan takarar biyu na zuwa ne yayin da Amurkawa ke shirin kada kuri'a a ranar 5 ga watan Nuwamba.