Trump Da Biden Sun Yi Muhawarar Karshe Kafin Zabe

Muhawar Shugaba Donald Trump da Joe Biden ta karshe

Yan takarar Shugaban kasar Amurka sun bayyana abinda ya banbanta su da kuma yadda za su tinkari muhimman matsalolin da suka tsonewa Amurkawa Ido

Shugaban Amurka Donald Trump na jam’iyyar Republican da mai kalubalantarsa dan takararar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat Joe Biden, a daren jiya Alhamis sun fafata a muhawarar karshe kafin zaben shugaban kasa na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Cikin manyan batutuwan da suka tattauna akwai batun yaki da cutar coronavirus da sauyin yanayi da tsaron kasa da batun iyalan Amurka da tsaron kasa da kuma batun nuna banbancin launin fata a Amurka.

Shugaba Donald Trump yana bayani yayin muhawara

Da aka yiwa ‘yan takarar tambayar ta wacce hanya zasu jagoranci kasar wajen kawo karshen annobar corona virus, sai Trump Ya ce “Kamar yadda aka sani, an yi hasashe mutum miliyan 2.2 aka sa ran za su mutu. Mun kuma rufe gawurtaccen tattalin arzikinmu domin mu yaki wannan mummunar cutar da ta fito daga China. Annoba ce da ta shafi fadin duniya, mun ga karuwar cutar a Turai da sauran wasu wurare. Idan aka lura za a ga yawan mutanen da cutar ta ke kashewa ya yi kasa da kashi 85 cikin 100.”

Da yake maida martani dan takarar jam’iyyar Democrat, Joe Biden ya ce “muna koyar yadda zamu yi rayuwa da ita. Mutane na koyon yadda zata kashe su. Ku mutanen dake gida zaku kasance da kujera babu kowa a kai da safe. Wannan matar ko miji da zasu je kwanciya za su yi yunkurin taba miji ko matarsu kamar yadda suka saba, zasu ji babu kowa. Mu koyi yadda zamu yi rayuwa da ita, haba, tana kashe mu dai.”

Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden yana bayani yayin muhawara

‘Yan takarar biyu wadanda dukansu suka ba shekaru 70 baya, sun rika sa baki lokacin da dayan ke Magana yayin muhawarar sai dai bai yi muni kamar yadda su ka yi makonni uku da suka shige ba, galibi sabili da hukumar da ke tsara muhawara tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa ta rika rufe na’urar Magana na ‘yan takaran na tsawon mintoci biyu lokacin da dayan ya fara bayani a kan muhimman batutuwa shida da aka yi muhawara a kai, yadda kowanne zai samu ya yi bayani ba tare da abokin hamayyar sa ya tsoma baki ba.

Miliyoyin Amurkawa sun riga sun tsaida shawara kan zaben, inda sama da mutane miliyan 47 suka riga suka kada kuri’unsu domin gudun yin gaba da gaba da sauran masu kada kuri’a a wannan yanayin da ake fama da annobar coronavirus.

Mutane suna kallon muhawarar daga cikin motocinsu

Biden ya yi zargin cewa dangataka tsakanin jinsuna ta kara tabarbarewa karkashin shugabancin Trump. Sai dai shugaban kasar ya fada kamar yadda ya saba cewa, babu shugaban kasar Amurka, mai yiwuwa, banda Abraham Lincoln wanda ya ‘yantar da bayi a karni na 19 , da ya kyautatawa bakaken fata kamar yadda ya yi.

Trump ya caccaki Biden da goyon bayan kafa dokar shekara ta 1994 da ta bada damar kulle tsirarru sabili da laifukan da suka jibinci miyagun kwayoyi. Biden ya amince da haka sai dai ya ce an yi kuskure da kafa dokar ya kuma ce ya yi kokarin ganin an yi gyara.

Kristen Welker da ta jagoranci muhawarar Trump da Biden

trump-da-biden-sun-kara-kaimi-a-wurin-kempe-a-jiya-lahadi

trump-da-biden-sun-yi-musayar-zafafan-kalamai-a-muhawararsu

muhawarar-mataimakan-yan-takarar-shugaban-kasar-amurka

mata-sun-gudanar-da-gangamin-kira-a-fita-zabe-a-fadin-amurka