Trump Bashi Da Cikakkiyar Tarbiyyar Da Zai Iya Shugabancin Amurka

Donald Trump Da James Comey

Tsohon shugaban Hukumar Binciken Manyan Laifukka ta Amurka ta FBI, James Comey yace shugaba Donald Trump baya da “cikakkiyar tarbiyya da kamun kan da zai iya shugabancin Amurka, kuma akwai shedar dake nuna cewa shugaban ya taba yunkurin hana doka tayi aikinta.”

Haka kuma Comey ya zargi shugaba Trump da cewa “shi ba mai iya fadar gaskiya bane.”

Duk wadanan kalaman na Comey suna zuwa ne a cikin hirar da tashar telbijin ta A-B-C tayi da shi ne a jiya, yayinda ake dab da fitowa da wani sabon littafin da ya rubuta da zai nuna rawar da ya taka wajen binciken rawar da Rasha ta taka a zaben shugaban kasan Amurka na shekarar 2016 da wanda ya gudanar game da sakkonin email na ‘yar takara jam’iyyar Democrats watau Hilary Clinton da kuma zantawarsa da shugaba Trump a bara kafin shi Trump din ya kore shi daga mukaminsa na shugabancin FBI.

Trump dai ya musanta akasarin duk wadanan zarge-zargen na Comey, ciki harda wanda yayi na cewa ya kori Comey ne don ya ki tsaida binciken da yake yi akan tsohon mashawarci kan harkokin tsaro, Michael Flynn.