Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Cafke Wasu ‘Yan Adawa Dake Zanga-zanga


 'Yan adawa da gwamnatin Nijar ta cafke
'Yan adawa da gwamnatin Nijar ta cafke

Ficewar jam’iyyar MPN ta fara nuna alamar baraka cikin kawance jam’iyyun da suke cikin gwamnatin PNDS, sai kuma gashi yau an cafke wasu shuganannin wasu jam’iyyun da kungiyoyi saboda suna zanga zangar kin amincewa da jibge sojojin kasashen waje cikin kasarsu

A Jamhuriyar Nijar da alama harkokin siyasa sun fara tabarbarewa soboda cafke wasu ‘yan adawa da suka shiga yin zanga-zangar da hukumomi suka ce haramtattiya ce.

Shugaban hadakar kungiyoyin da suka shiga zanga zangar, Gamace Mahammadou ya tabbatar da cafke wasu ‘yanuwansu tare da cewa shi kansa yaji hukumomi na nemansa.

Dangane da wadanda aka cafke irin su Diori Ibrahim da Maykol Zodi Gamace Mahammadouya ce basu tantance inda suke ba amma kuma su ba zasu yadda da mulkin kama karya ba a kasarsu.

Injishi ba zasu yadda a kawo masu sojojin wasu kasashen waje a jibegesu cikin kasarsu ba.

Duk da cewa hukumomin Yamai sun sanar dasu cewa zanga-zangarsu haramtaciya ce, mai magana da yawun kungiyoyin ya ce hanasun tamkar mulkin danniya ne da su bazasu amince dashi ba. A cewarsa zasu yi gwagwarmaya sosai domin su kwato ‘yancin kasarsu.

Akan ko shi kansa zai gudu ko ya boye saboda ana nemansa, sai ya ce shi ba zai gudu ba. Yanzu ma suka fara fafutika ta gasken gaske saboda wai kasar tasu ce.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG