Shugaba Amurka Donald Trump, ya ce "idan wani abu ya faru", a kasar kada su ga laifin kowa illa alkalin da ya dakatar da aiki da dokar da ta hana shigowa Amurka daga al'umar kasashe bakwai wadanda akasarin jama'ar su Musulmi ne.
WASHINGTON, DC —
A daya daga cikin sakonnisa da ya wallafa a shafin Twitter a jiya Lahadi, shugaban ya ce "Gaskiya na gaza fahimtar yadda alkali zai jefa kasarmu cikin hadari."
A karshen makon da ya gabata ne, alkalin wata kotun Amurka James Roberts a jahar Washington ya dakatar da aiki da dokar shugaban kasar na wucin gadi. Sannan a jiya Lahadin, kotun daukaka kara dake shiyya ta tara a San Francinsco ta ki amincewa da bukatar da gwamnatin Trump ta gabatar na neman kotun ta ba da izinin a ci gaba da aiwatar da dokar.
A ci gaba da sakonni n Twitter a jiya Lahadi, Mr. Trump ya ce ya umarci ma'aikatar tsaron cikin gida ta "binciki masu shigowa Amurka sosai". Ya kara da cewa alkalin ya sa aikin masu kula da shige da fice cikin wani kangi."