Shahararren kamfanin kera motoci a duniya “Toyota Motor Corp” ya bayyana kudirin sa na kerawa da sayar da motoci masu magana da juna a kasar Amurka nan da shekarar 2021, kamfanin na kasar Japan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin.
Motocin zasu rika ganawa da juna ta tsarin yanar gizo, wanda hakan zai kawo raguwar hadurra akan tituna, musamman a wajajen mahada, idan mota ta matsi ‘yar’uwarta, zata shaida mata cewar ina kusa don haka ki kara nesanta kanki dani domin kada mu gogi juna.
Kamfanin dai na sa ran gwamnatin Amurka ta aminta da tsarin maganar motoci a tsakanin su, don fara aikin motocin a shekarar 2020, ya zuwa yanzu dai an gwada wannan tsarin na motoci masu magana da juna, wanda ya samu nasara.
Hakan ya kara tabbatar da cewar idan aka samar da tsarin, zai taimaka wajen rage yawaita hadurra akan manya-manyan tituna a koina a kasar, hukumar kula da manyan tituna ta Amurka ta tabbatar da cewar za’a samu raguwar hadari da zai kai na yawan motci 600,000 a kowace shekara, idan ana amfani da motoci masu magana da junan su.
Kuma za’a samu raguwa a irin yawan dukiya da ake rasawa da zasu kai kimanin dallar Amurka Billiyan saba’in da daya $71B. Kamfanin zai bayyanar da sauran bayanai akan tsarin motocin kamin nan da karshen wannan shekarar.