Matashin dan kwallon nan na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Tosin Kehinde ya yanke shawarar buga wa Najeriya, wasa a matakin kasa da kasa.
Dan wasan mai shekarun haihuwa 19, wanda ya cancanci buga wasa a Ingila, an nuna hotunansa yana gaisawa da mai horas da kungiyar Super Eagles na Najeriya, Gernot Rohr a wasan da suka buga a London tare da Serbia, a makon da ya wuce kuma ya tabbatar da cewa ya zabi Super Eagles a matsayin kungiyar sa.
Ya kuma ce Najeriya, ta kasance wani ɓangare na san a musamman. Kehinde ya shaida wa kafar sadarwar BBC. "An haife ni a can, ‘yan uwana duka na Najeriya ne. Na fito ne daga wata zuriya mai karfi a Najeriya”.
Kehinde ya samu shiga atisaye da manyan ‘yan wasn Manchester United, a karon farko a kakar wasa ta bana kuma ya buga wasanni 15 a ‘yan kasa da shekaru 23 na Manchester united.
Har ila yau Wani matashin dan wasan Chelsea wanda ba a bayyana sunan sa ba a Ingila zai iya kasancewa a tawagar ‘yan wasan Najeriya, a nan gaba.
An ce dan wasan ya fara tattaunawar sirri tare da jami'an kula da wasa na kasa a hotel a London kafin wasan Najeriya da Serbia, wanda ya gudana a satin da ya gabata.