Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA zata dubi gaskiyar abinda ya faru na nuna wariyar launin fata a wasan da Faransa ta samu nasara a kan Rasha da kwallaye 3-1 a wasan sada zumunta da akayi a cikin makon nan
Hukumar kula da wasan na duniya ta ce a cikin wata sanarwa da suka samu sun "tattara rahotanni daban-daban da ke shaida mai yiwuwa" na nuna bambanci ga dan wasan.
Manchester United, Paul Pogba da kuma Ousmane Dembele, na Barcelona.
Tawagar ‘yan wasan kwallon Kafa na mata na kungiyar Chelsea ta kai ga wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai bangaren mata a karon farko bayan ta doke Montpellier da ci 3-1 da ci 2--0 a gida wanda hakan ya bata jimillar kwallaye 5-1.
Itama tawagar mata ta Manchester City ta kai ga wasan Kusa da na karshe dukkan kungiyoyi biyu na Ingila suna nuni da cewa akwai kulob din Burtaniya biyu a cikin' wasan kusa da na karshe a karo na farko a tarihin wasan bangaren mata.
Chelsea da Wolfsburg zasu hadu a wasan dab da na karshe sai kuma Manchester City da Lyon masu rike da kofin.
Dan kwallon Leicester City, Kelechi Iheanacho bai fafata a wasan sada zumunta da kasar Serbia, ta doke Najeriya da ci 2 -0 sakamakon karayar kashi a hannunsa a ranar Talata, kocin Super Eagles Gernot Rohr ya bada tabbacin hakan. Kungiyar Leicester ta na shirin duba shi kafin ranar Asabar dazata fafata da Brighton a gasar Firimiya lig na kasar Ingila.
Facebook Forum