Tony Elumelu Ya Tallafawa Masu Kananan Sana'oi Dubu Daya

A wannan mako dandalinVOA ya sami hallartar taron tallawafawa masu kananan sana'oi guda dubu daya da gidauniyar Tony Elumelu kan shirya wa matasa a fannin sana'oi mutane dubu daya a sassan kasashen Afrika a duk shekara da aka gudanar a jihar Lagos.

A wannan karo ana shekara ta uku, da fara wannan taro kuma matasa 1000 suka ci gajiyar wannan shiri da dala dubu biyar biyar kowannensu - ko daya yake wannan tallafi na fitowa ne daga aljihun ‘yan kasuwa sai wasu kamfanoni masu zaman kansu.

Wasu da suka ci gajiyar shirin a nan gida Nijeriya da ma jamhuriyar Nijar sun bayyana irin sana’oinsu da ma abinda zasu yi da tallafin dala dubu biyar da suka samu.

Mai gayya mai aiki attajiri Tony Elumelu ya bayyana dalilin wannan shiri nasa da ya ware shekaru goma don tallafawa masu kananan sana’oi

Fatan Tony Elumelu dai shine tabbatar da kasuwancin ‘yan Afrika ga mutanen Afrika tare da samar da ayyukanyi ga duban matasan da suka ci gajiyar shirin inda suma zasu dauki wasu matasan don bunkasa musu rayuwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Tony Elumelu Ya Tallafawa Masu Kananan Sana'oi Dubu Daya