WASHINGTON, DC —
Tsohon kwach na kungiyar FC Barcelona, Tito Vilanova, ya rasu yau jumma'a.
Vilanova ya rasu yana da shekaru 45 da haihuwa a sanadin cutar sankara.
Magoya bayan FC Barcelona da masu sha'awar kwallo ba zasu manta da mutumin da ya jagoranci kungiyar ta lashe wasannin lig-lig na La Liga da maki 100 ba, wanda kuma har kungiyarta ta matasa ya koyar.
Vilanova, dan wasan tsakiya, ya buga a kungiyar matasa ta FC Barcelona na tsawon shekaru biyu, amma ya fi shahara a wasannin da yayi da kananan kungiyoyi irinsu Figueres, Lleida, Badajoz, Elche da Gramanet. A tsakiyar shekarun 1990, ya buga a lig na Primera tare da kungiyoyi irinsu Celta Vigo da Mallorca.