Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanene Zai Gaji David Moyes A Manchester United? Ga Sunayen Wasu - 23/4/2014


A bayan da Manchester United ta sallami David Moyes, yanzu rade-radi yayi yawa a kan ko wanene zai gaje shi a kan wannan kujera ta Manaja. Ga sunayen wasu daga cikin wadanda ake rade-radin:

Da farko dai Ryan Giggs, tsohon dan wasan United, wanda aka ba rikon wannan kujera a yanzu. Zai ci gaba da rike ta a bayan wannan kakar kwallon kafa, ko kuma dai rikon kawai zai yi kafin a nada wani?

Louis van Gaal – ‘yan Manchester United da dama su na kwadayin ganin van Gaal ya karbi ragamar kulob dinsu, duk da cewa bai taba yin wasa ko koyarwa a Ingila ba. Sai dai ya sha yawo kam! Ya jagoranci Ajax, FC Barcelona, kungiyar kasar Netherlands, FC Barcelona a karo na biyu, ya sake komawa Netherlands ya kuma dawowa Barcelona. Daga nan ya yi manaja a AZ Alkmaar da Bayern Munich. Gidan telebijin na ESPN ma yace tuni har United ta tuntubi van Gaal.

Jurgen Klopp – Akwai rahotannin dake cewa manajan kungiyar kwallon kafar ta Dortmund, ya fito yace babu ta yadda zai karbi aikin manajan Manchester United, ‘yan sa’o’I kadan bayan korar David Moyes. Abubuwa su na iya canjawa dai kam. Akwai ma rade-radin cewa kungiyoyi irinsu FC Barcelona da Tottenham su na kwadayin janyo wannan manaja mai shekaru 46 da haihuwa.

Diego Simeone – Anya akwai ta yadda Atletico Madrid zata iya rabuwa da wannan manaja nata dan asalin kasar Argentina? Simeone, mai shekaru 43 da haihuwa, ya samu nasarar kai Atletico Madrid zuwa ga wasannin kusa da karshe na cin kofin zakarun kulob na Turai, kuma watakila zai yi kwadayin karbar ragamar kulob wadda ba a fagen kwallon kafa kawai ba, a duk ma kungiyoyin wasanni, babu kama da ita.

Sauran dai sun hada da Roberto Martinez, Mauricio Pochettino, Clarence Seedorf, Roberto di Matteo, Carlos Quieroz, Carlo Ancelotti, Pep Guardiola. Ga su nan dai barkatai.

Abinda kawai ya tabbata shi ne cewa ko ma wanene Manchester United ta zabo ta ba kujerar manajanta, zai zamo babban labari a dukl fadin duniya.
XS
SM
MD
LG