Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da jawabi a gaban hadakar zaurukan majalisun tarayyar kasar a gobe Laraba, 29 ga watan Mayun da muke ciki.
A sanarwar daya fitar, Akawun Majalisar Tarayyar, Sani Tambuwal, yace shugaban kasar zai yiwa 'yan majalisun jawabi ne game da halin da kasa ke ciki tare da kaddamar da dakin karatun majalisar.
An ruwaito sanarwa na cewar, "muna sanarda masu girma 'yan majalisar dattawa dana wakilai cewar, a wani bangare na bikin murnar cika shekaru 25 ba tare da tsarin dimokradiya dana majalisun dokoki ya yanke a Najeriya ba, za'a a gudanar da zaman hadin gwiwa na zaurukan majalisun tarayya 2 a gobe laraba 29 ga watan mayun da muke ciki".
"Shugaban kasa Bola Tinubu zai gabatar da jawabi ga hadakar zaurukan majalisun tarayya 2 akan halin da kasa ke ciki tare da kaddamar da dakin karatun majalisar kasa".
"Ana sa ran masu girma 'yan majalisar su kasance a wuraren zamansu da misalin karfe 9 na safiya".
Shugaban Kasa Bola Tinubu, da aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, zai yi bikin cikarsa shekara guda akan mulki a gobe Laraba.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta bijiro da sauye-sauyen da suka hada da janye tallafin man fetur da hade harkar canjin kudaden ketare a wuri guda saidai tana cigaba da yaki da illolin hakan da suka bayyana a matsayin hauhawar farashi da tsadar rayuwa.