Janar Christopher Musa ya tabattar da hakan ne yayin wata hira ta musamman da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, a Abuja, birnin tarayyar Najeriya, inda ya zayyana matakan da su ke dauka na shawo kan wannan matsalar.
Bisa ga cewar sa, taimako daga Allah da kuma hadin kan da su ke samu daga jama’a sun taimaka gaya. Ya kuma bayyana cewa, ya kamata mutane su sani cewa akwai miyagun mutane a tsakanin al'umma da ke karban kudin jini, kuma tilas ne a yi masu iyaka idan ana son ganin bayan ayyukan su.
Ya kuma nuna bakin cikinsa ganin yadda lamarin ya fi shafar arewacin Najeriya.
Ya kara da cewa cikin shekara dayan da aka cika karkashin mulkin shugaba Tinubu, an samu nasarar samun kwanciyar hankali a wuraren da ake fuskantar matsolin tsaro, yayinda aka kuma samu nasarar kubutar da yaran da aka yi garkuwa da su a sassa daban daban na kasar.
Janar Christopher MusaYana yace, fatansu shi ne su ga manoma sun koma noma kuma jama'a sun koma gidanje su ko kuma kasuwanci cikin kwanciyar hankali.
Saurari wannan bangaren hirar:
Dandalin Mu Tattauna