A ranar Alhamis 23 ga watan Mayu nan ne shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin N’Djamena na Jamhuriyar Chadi domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Idriss Mahamat Deby Itno.
WASHINGTON, D. C. - Bikin rantsar da shi ya biyo bayan ayyana shugaba Deby a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon watan Mayu da kotun tsarin mulkin kasar ta Chadi ta tabbatar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, wasu manyan jami’an gwamnati ne za su raka shugaba Tinubu kuma zai dawo bayan kammala bikin.
Deby, shugaban mulkin sojan Chadi, ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu ne, da kashi 61 na kuri'un da aka kada, a cewar sakamakon karshe da aka sanar.
Sai dai babban abokin hamayyarsa Succes na kalubalantar sakamakon zaben.