Lawal na magana ne bayan wani taro da ya ce sun gudanar da wasu manyan masu ruwa da tsaki don shirya kawar da gwamnatin Tinubu a zaben 2027.
In za’a tuna Babachir wanda shi ne madugun nemawa Tinubu tikitin takarar APC a 2023, ya raba gari da shi ya marawa dan takarar LEBA Peter Obi baya.
Babachir Lawal ya ce ya tabbatar ‘yan arewa a yanzu sun gane togaciyar da yake yi musu kan rashin wani tanadi gare su daga Tinubu “wane irin gwamnati haka ba ruwan ta da jama’a sai surutu, gwamnati an cika da ‘yan Legas.”
Da yake martani mai ba wa shugaba Bola Tinubu shawara kan siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya ce shi a gare shi Babachir hauragiya ya ke yi “mutum ne da dama ta same shi ta kubce masa, yana cikin mutane da a ka ce ya da ce a tausaya mu su.”
Babachir a zantawar ya ce duk sharuddan faduwar gwamnatin Tinubu a zabe mai zuwa sun cika “mun tuba indai laifin mu ne, zunubin mu ya sa Allah ya yi ma na haka to mun tuba ba za mu kara ba.”
Amma a na sa bangaren Ibrahim Masari ya ce dama ai ba da kuri’ar Babachir suka lashe zabe ba “abu ya zama zuciya ba kyau Allah ya gwada masa iyakar shi, jiya ma me ta yi ballantana yau.”
A zahiri dai akwai wasu manyan jiga-jigan da ke APC gabanin zaben 2023 amma yanzu sun koma danyen ganye da bangaren hamayya duk da minista Nyesom Wike da ya bude da cewa har yanzu ya na PDP na yi wa babbar lemar adawar sakiyar da ba ruwa.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5