Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Justice Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar babbar mai shari’a ta Najeriya bayan da Babban Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya.
Washington D.C. —
Tinubu wanda ya dawo daga ziyarar da yai kai Faransa, ya rantsar da alkaliyar ne da safiyar Juma’a a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
‘Yar shekaru 66, Kudirat ta zamanto mace ta biyu da ta rike wannan mukami inda ta maye gurbin Alkali Olukayode Ariwoola wanda ya yi ritaya a ranar Alhamis.
Shekarun Ariwoola biyu a mukamin.
Majalisar Alkalan Najeriya ce ta mika sunan Justice Kekere-Ekun a matsayin babbar alkaliyar da za ta jagorancin ofishin.
A watan Yulin shekarar 2013 aka karawa Kekere-Ekun matsayi zuwa Kotun Kolin kasar inda ta zama mace ta biyar da ta taba zama mai shari’a a kotun.