Shugaban Najeriya Bola Tinubu da takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa sun gudanar ta wata tattaunawa bayan kammala bikin karbar rantsuwar kama aikin da Ramaphosan yayi.
A yau Alhamis, hadimin Shugaba Tinubu Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X cewar, Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da Bola Tinubu na Najeriya sun gudanar da tattaunawar kasa da kasa akan harkokin diflomasiya da tattalin arziki bayan kammala bikin rantsar da ramaphosan.
Shugaban Najeriya ne ya karbi bakuncin taron a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudun.
A sanarwar daya fitar bayan kammala ganawar, mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya ruwaito mai gidansa na cewar, “naji dadin jawabin daka gabatar yayin bikin. Sauraronka ya faranta raina. Muna da dimbin matsaloli iri daya, don haka muna bukatar yin aiki tare da juna. Wannan biki yayi kyau kwarai.”
Shima shugaban Afrika ta Kudun ya jinjinawa Tinubu daya samu sukunin halartar bikin rantsar dashi.
An ruwaito shi yana cewar, “ina gode maka matuka daka halarci bikin rantsar dani. Naji dadin ganin danuwa na a yayin bikin”.
An rantsar da Ramaphosa ne a jiya Laraba bayan kulla yarjejeniyar kafa gwamnatin gambiza tsakanin jam’iyyar ANC da wadansu jam’iyyu.
Tinubu na cikin jerin shugabannin da suka halarci bikin rantsar da Ramaphosa, saidai wani faifan bidiyo ya karade shafukan sada zumunta dake nuna yadda shugaban Afrika ta Kudu yaki martaba Tinubu a bikin