Shugabanni a Najeriya na ci gaba da mika sakonnin ta’aziyyarsu bisa ibtila’in fashewar tankar mai da ya auku a yankin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Sama da mutum 100 ne aka tabbatar da mutuwarsu a lokacin da gobarar ta tashi a jikin wata tankar mai da ta fadi a ranar Laraba a yankin na Majia.
Akwai kuma fargabar adadin zai iya karuwa yayin da aka kwantar da mutum sama da 90 a asibiti da kuna iri-iri.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga al’umar jihar ta Jigawa inda ya ba da umarnin tura wata tawaga zuwa jihar don jajantawa gwamnati da al’umar jihar.
“Tawagar gwamnatin za ta kunshi Ministan Tsaro Muhammadu Badaru Abubakar, Ministan Sufuri, Sanata Saidu Alkali, Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta FRSC, Shehu Muhammad, Mai bai wa Shugaba shawara kan al’amuran da suka shafi hulda da al’umomi shiyyar Arewa maso Yamma, Abdullahi Tanko Yakasai.” Wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu Bayo Onanuga ya fitar ta ce.
Ga sauran sakonnin jajen da sauran shugabannin siyasar Najeriyar suka fitar bayan aukuwar lamarin:
“Wannan babban abin alhini ya jijjiga mu matuka. Gwamnatin Tarayya na tare da al’umar jihar Jigawa. Muna kan tattaro dukkan taimako don tallafawa wadanda suka jikkata tare da taimakawa iyalan wadanda wannan al’amari ya shafa.” In ji Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima.
Yayin da shi ma yake mika sakon ta’aziyyarsa, Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kwatanta al’amarin a matsayin mai sosa rai tare da ba da shawara kamar haka:
“Ya zama wajibi ya horar da direbobin da ke safarar mai a kuma duba tsare-tsaren safararsa da yadda ake jigilar man fetur da sauran dangoginsa. Lokaci ya yi da za mu fara duba tsarin jigilar mai ta jirgin kasa a sassan kasar nan.” In ji Atiku.
“Wannan dabi’a ta zuwa kwasar mai da take yawan faruwa a wuraren da aka yi hatsarin tankar mai na ci gaba da lakume rayuka. Babu haufi, kuncin rayuwa ya tsananta, a dalilin tsananin talauci, mutanenmu kan jefa kansu cikin mummunan hadari a yunkurinsu na ganin sun rufawa kansu asiri.” In ji dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi.
Yayin jajensa, shi ma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso shawara ya bayar irin ta Atiku kan yadda ya kamata a rika safarar man fetur a cikin Najeriya.
“Yayin da nake addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu a wannan hadari, Ina kira ga wadanda safarar mai ya rataya a wuyansu a kasar da su bullo da wata hanya mara hadari da za a rika jigilar duk wani abu mai hadari. Ya zama wajibi mu kiyaye asarar rayukan mutane a nan gaba.” In ji Kwankwaso.