Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Mutanen Da Hadarin Tankar Mai Ya Yi Ajalinsu


Tankar Mai
Tankar Mai

Hukumomin a jihar Jigawa sun gudanar da jana’izar wadanda suka mutu a wani mummunan hatsari da ya afku a safiyar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024, inda wata tankar mai ta fashe a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, ta yi sanadin mutuwar mutane 94 tare da jikkata wasu 50.

Lamarin ya faru ne lokacin da wata tankar mai da ta taso daga Kano zuwa Yobe ta rasa yadda za ta yi, ta kife a kusa da jami'ar Khadija da misalin karfe 12:30 na safe.

A cewar rahotannin ‘yan sanda, fashewar ta tashi ne a lokacin da mazauna yankin suka garzaya wurin da abin ya faru, inda aka zarge su da yunkuri domin dibar man fetur din da ya zube.

Gobarar da ta tashi ta lakume dandazon jama’a, lamarin da ya kai ga wata mummunar gobara da ta kashe akasari a nan take.

An ruwaito cewa tankar ta yi kusan awa sa'o'i tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG