A ziyararsa ta farko a Kyiv a yau dinnan Lahadi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya ce Amurka ta gaya ma Rasha cewa dole ne fa ta dau mataki na farko na kawo karshen tashin hankali a Gabashin Ukraine.
Tillerson ya yi jawabin ne ganga da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko bayan da mutane biyun su ka gana don tattauna yadda za a kawo karshen tashin hankali a Gabashin Ukraine ta kuma goyi bayan kokarin Ukraine na sauye-sauye.
"Ina da kwarin gwiwar cewa muddun wadanda abin ya shafa su ka dukufa ga cimma wannan burin, za mu samu cigaba," a cewar Tillerson, yayin da ya ke nuni da yarjajjeniyar da aka cimma a Minsk - wadda yarjajjeniya ce ta kwance damara da Rasha da Ukraine su ka cimma a 2015.
Tillerson ya nada tsohon Jakadan Amurka a kungiyar Kawance ta NATO Kurt Volker a matsayin wakili a tattaunawa kan Ukraine.