Tiger Woods Na Samun Sauki

Tiger Wood

Tiger Wood

Aikin tiyatar da aka yi wa fitaccen dan wasan golf din Amurka Tiger Woods ya yi nasara kuma yana samun sauki, a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na Twitter.

A ranar Laraba Woods ya yi wani mummunan hatsari wanda ya sa motarsa ta wuntsula ta fada cikin wani rami a birnin Los Angeles.

Sanarwar an wallafa ta ne a ranar Juma’a wacce ta yi karin hasken cewa, an gudanar da aikin an kuma mayar da shi asibitin Cedars-Sinai Medical Center.

“An yi nasara a aikin, kuma yana samun sauki tare da koshin lafiya” Sanarwar ta ce.

“Tiger Woods da iyalansa suna mika godiyarsu ga kowa da kowa dangane da sakonnin fatan alheri da aka aika mana cikin ‘yan kwanakin nan.”

Bayan da ya yi hatsarin, an garzaya da Woods asibitin Harbor- na UCLA, domin yi masa maganin raunukan da ya ji.

Shi kadai ne a cikin motar a lokacin da hatsarin ya auku yayin da bayanai suka yi nuni da cewa ya ji rauni ne a kafarsa.

Dan shekara 45, Woods ya je yankin na Los Angeles ne domin halartar wata gasar Golf ta PGA Tour da wata gidauniyarsa ke daukan nauyi.

Woods wanda sau 15 yana lashe manyan gasar golf, bai buga wani wasa ba saboda yana murmurewa daga aikin da aka yi masa a baya a ranar 23 ga watan Disamba.