Tawagar da shugaban ya aika ta bayyana jimami tare da alhinin da shugaban kasa ya yi game da kisan gillar da aka yi wa manoman shinkafa 43. Haka kuma shugaban kasa ya baiwa rundunar tsaron kasar umarnin gudanar da bincike don gano mutanen dake da hannu a ta’asar.
Gwamnatin Najeriya ta dauki tsauraran matakan ganin abin da ya faru a kauyen Zabarmari bai sake faruwa a kasar ba, a cewar tawagar.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi kira ne ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara taimaka wa al’ummar Borno. Inda ya ce, a taron gwamnonin shiyyar arewa maso gabas da aka gudanar a jihar Adamawa, sun lura da cewa Naira Biliyan 45 ne kadai aka ware ga jihohin wanda hakan ba zai yi wani tasiri ba ga tsaron yankin.
Haka kuma gwamna Zulum ya bayyana kin amincewarsa da kafa kwamitin binciken cin zarafin da 'yan sanda suka yi a jihar, ganin cewa gwamnatin tarayya ba ta kafa wani kwamiti na ganin an binciki kashe-kashen da kungiyar Boko Haram ke yi ba.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5