Tawagar Shugaba Muhammad Buhari ta kai ziyara makarantar Chibok

Wasu iyayen 'yan matan Chibok suna kuka da ihu saboda 'ya'yansu da Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata

A tunawa da sace 'yan matan makarantar sakandare ta mata dake Chibok shekaru biyu da suka gabata, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya aika ta tawaga zuwa garin domin jajantawa iyayen yaran tare da basu tabbacin kwatosu daga hannun 'yan Boko Haram da suka sacesu.

Tawagar da ta isa makarantar ta gamu da koka da ihun iyayen 'yan matan da yanzu suka kwashe shekaru biyu suna jiran gwamnati ta kwato masu 'ya'yansu.

Tawagar a karkashin jagorancin Amina Muhammad ministar ma'aikatar muhalli ta je Chibok din ne domin jajantawa iyayen 'yan matan da aka sace tare da basu hakuri. Tace zasu fitar da sakamakon binciken da aka yi da wanda za'a yi kowa ya san gaskiya saboda haka iyayen su kara hakuri. Za'a kawowa garin Chibok ayyuka da wasu taimako domin kwantar da hankulan mutanen garin musamman iyayen da aka sace 'ya'yansu.

To saidai iyayen sun nuna matukar damuwa da bacin ransu dangane da rashin sanin makomar 'ya'yan nasu shekaru biyu da sacesu.Wani wakilin iyayen Yakubu Kese yace abun dake basu haushi shi ne yadda wasu da suka san abun da zai faru aka cire masu 'ya'yansu kafin a sace sauran. Yace suna da masaniyar abun da ya faru. Duk matakan gwamnatoci uku wato karamar hukuma da jiha da tarayya duk sun san abun da ya faru.

Amma gwamnan jihar Kashim Shettima ya maida martani akan furucin na Yakubu Kese.'Ya'yansu hamsin da bakwai da suka kubuta daga hannun kungiyar Boko Haram ba gwamnatin tarayya ta dauki nauyin ilimantar dasu ba. Gwamnatin jiha ce kuma nera miliyan hamsin gwamnatin jihar ta kashe. Yace 'yan matan 41 dake kiristoci ne sun kaisu makaranta a Jos jihar Filato kana 14 dake musulmai an kaisu makaranta a wani garin daban. Gwamnan ya ki ya fadi sunayen makarantun da suke saboda dalilan tsaro tare da kira a girmama juna.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tawagar Shugaba Muhammad Buhari ta kai ziyara makarantar Chibok - 4' 39"