Wata tawagar manyan jami’ai daga Eritrea ta isa makwabciyarta Habasha domin fara wata tattaunawa mai cike da tarihi a kan kawo karshen daya daga cikin yaki mafi dadewa a Afrika.
Tawagar ta Eritrea ta isa birnin Addis Ababa ne a jiya Talata.
A makon da ya gabata ne shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya yi alkawarin aikewa da tawagar, a lokacin da kasarsa take bukin tuna mazan jiya a babban birnin kasar Asmara. Alkawarin na shugaba Afwerki wani martani ne ga alkawarin da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi a farkon wannan wata cewa zai mutunta ka’idodin yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2000 domin kawo karshen yakin shekaru biyu a kan iyakokin kasashen.
Habasha ta dade bata amince da ka’idodin yarjejeniyar ba, da ta hada da janyewar Habasha daga garin Badme dake kan iyaka.
Eritrea tsohon lardi a cikin Habasha, ta balle ne a shekarar 1993.