Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Habasha da Somaliya Za Su Iganta Dangantakarsu


Sabon Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed
Sabon Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed

Bayan dan tsami da dangantakar kasashen Habasha da Somaliya ta yi, Shugabannin kasashen na yanzu sun sha alwashin karfafa cudanyar kasashen biyu.

Sabon Firaministan Habasha Abiy Ahmed da Shugaban kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Farmajo, jiya Asabar sun amince su inganta dankon zumuncinsu tare da hada kai da kungiyar Tarayyar Afirka, wajen neman mafitar matsalolin da ke addabar nahiyar.

Bayan tattaunawa ta bai daya jiya Asabar a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, Shugabannin biyu sun fada a wata takardar bayani cewa kasashen biyu, za su habbaka dangantakar diflomasiyya da kuma ta cinakayya tsakaninsu, ciki har da bude ofisoshin jakadanci da kuma kawar da abin da su ka kira, "dukkannin shingogi na cinakayya da tattalin arziki."

Da Ahmed da Farmajo sun yi Allah wadai da duk wani nau'i na ta'addanci, su na masu jaddada muhimmancin hada kai wajen dakile ta'addanci da kuma tinkarar kalubalen tsaro a kan iyakokinsu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG